Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha kuma wakilin shugaban kasar kan harkokin yankin gabas ta tsakiya Mikha’il Bogdanov ya gargadi gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kan ta guji ci gaba da gudanar da bakar siyasarta na bangare guda kan al’ummar Palasdinu da hakan zai kara dagula al’amura a yankin gabas ta tsakiya musamman shirinta na gudanar da gine-ginen matsugunan yahudawa ‘yan kaka gida a yankunan Palasdinawa da kuma tsare kudaden hukumar cin gashin kan Palasdinawa.
Bogdanov ya kuma bayyana cewar gwamnatin Rasha zata ci gaba da gudanar da duk wani kokari domin ganin an kai ga warware rikicin Palasdinawa da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta hanyar tattaunawa da bangarorin biyu ko kuma ta hanyar kungiyoyin kasa da kasa.ABNA.